Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya gana da firaministan kasar Finland Juha Sipilä a jiya, inda shugaba Xi ya ce, yayin da aka rage saurin habakar tattalin arzikin duniya, kasar Sin na ci gaba da bunkasa tattalin arzikinta yadda ya kamata.
Yayin ganawar da ta gudana a Helsinki, babban birnin kasar Finland, Xi Jinping ya ce, yanzu haka, kasar Sin tana zurfafa gyare-gyaren da take yi ga tsarin tattalin arzikinta.
Ya ce, Sin ta kware wajen tabbatar da bunkasar tattalin arzikinta yadda ya kamata, a kokarin da take na kara samar da zarafi da alheri ga kasashen duniya, ciki har da kasar Finland. (Tasallah Yuan)