Hakan dai na zuwa ne yayin da Shugaba Xi Jinping ke gudanar da ziyarar aiki a kasar Finland.
Yayin tattaunawar da Xi ya yi da takwaransa na Finland Sauli Niinisto a yau Laraba, shugabannin biyu sun nanata burin su na karfafa dadaddiyar alakar zumunta da hadin gwiwar kasashen su bisa yanayin da ake ciki yanzu haka, ta yadda al'ummun sassan biyu za su ci gajiyar wannan zumunci yadda ya kamata.
Bayan tattaunawar ta su shugabannin biyu sun sanya ido yayin rattaba hannu kan wasu takardun hadin kai a fannonin kirkire-kirkire, da dokokin shari'a, da na hadin gwiwar nazari kan dabbar panda da dai sauransu.
Baya ga haka, shugabannin biyu sun gana da manema labaru tare. (Saminu)