Wannan ce ziyarar farko da wani shugaba na kasar Sin ya gudanar zuwa kasar cikin shekaru 22 da suka gabata.
Kasar ta Finland ta kasance daya daga cikin kasashen yammacin duniya da suka riga sauran yammacin kasashen duniya kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin, kuma ita ce kasar yammacin duniya ta farko da ta rattaba hannu kan yarjejeniyar cinikayya da kasar Sin.
Kasashen biyu suna da dangantakar hadin gwiwa a fannonin da suka hada da fasahar zamani, makamashin marar gurbata muhalli, kirkire-kirkire da kuma fannin bincike kan yanayin sanyi, kana kasashen biyu suna da hadin gwiwa ta fuskar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu, wanda ake sa ran kasar Sin ce za ta karbi bakuncin gasar wasannin Olympic na lokacin hunturu a shekarar 2022. (Ahmad Fagam)