Cikin bayanin ya bayyana cewa, kasar Sin da tarayyar Turai manyan ginshikai biyu ne a fadin duniya. A kuma halin yanzu, dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Turai na bunkasa cikin sauri, musamman ma a fannonin wanzar da zaman lafiya, da neman ci gaba, da yin kwaskwarima, gami da raya al'adu.
Ya ce a halin yanzu, kasar Sin da kasashen Turai dukkansu na nuna azama wajen yin kwaskwarima ga manyan tsare-tsarensu, da habaka tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar al'umma. Bangarorin biyu na kara yin mu'amala dangane da dabarunsu na neman ci gaba, da samun moriya tare, lamarin dake da muhimmiyar ma'ana gare su.
Kaza lika shugaba Xi ya ce kamata ya yi Sin da Turai su ci gaba da kokari tare, wajen bayar da sabuwar gudummawa ga shimfida zaman lafiya da neman samun wadata a dukkanin sassan duniya.(Murtala)