in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an Sin da Amurka sun bayyana tattaunawar Xi da Trump a matsayin muhimmin batu game da hulda tsakanin kasashen biyu
2017-04-03 12:30:59 cri

Manyan jami'an Sin da Amurka sun bayyana tattaunawar da ake saran gudanarwa tsakanin shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Amurka Donald Trump, a matsayin muhimmin batu wanda zai kara karfafa dangantar da ke tsakanin kasashen biyu.

A wata zantawa ta wayar tarho da ya gudanar da sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, dan majalisar zartaswar kasar Sin Yang Jiechi, yace tattaunawar da za'a gudanar tsakanin shugabannin kasashen biyu, a halin yanzu shi ne babban batu mai girma wajen karfafa kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen biyu, kuma wannan al'amari yana da muhimmanci wajen bunkasa kyakkyawar fahimtar juna tsakanin Sin da Amurka a wannan yanayin da ake ciki, kana zai samar da wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali da cigaba a yankin Pacific da ma duniya baki daya.

Mista Yang yace, kasar sin tana fatan bagarorin biyu za su gana da juna, sannan a hannu gudu kuma, za su cigaba da yin hadin gwiwa tare domin tabbatar da ganin an cimma burin da aka sanya gaba.

Tillerson a nasa bangaren ya ce, shugaba Trump ya shirya tsab domin karbar bakuncin Xi a masaukin Mar-a-Lago dake jihar Florida ta Amurka.

Ya ce ganawar tsakanin shugabannin biyu dake tafe, tana da muhimmanci wajen karfafa dangantakar dake tsakanin kasashe biyu a nan gaba, ya kara da cewa gwamnatin Amurka ta sha alwashin daukar dukkanin matakan da suka dace wajen shirya tattaunawar, sannan a shirye take ta yi aiki tare da kasar Sin domin ganin tattaunawar ta haifar da kyakkyawan sakamako da ake fata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China