Kasar Sin na fatan tattaunawar da za a yi tsakanin Shugaba Xi Jinping da takwaransa na Amurka Donald Trump, zai bude wata hanya ta inganta dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Da yake jawabi ga manema labarai a yau Jumma'a, mataimakin ministan harkokin wajen Sin Zheng Zeguang, ya ce wannan shi ne karon farko da shugabannin biyu za su gana tun bayan da shugaba Trump na Amurka ya kama aiki.
A cewar Zheng, yayin ganawar, shugabannin biyu za su yi musayar ra'ayi kan dangantakar Sin da Amurka da muhimman batutuwa dake daukar hankalin yankunansu da duniya baki daya, da nufin inganta fahimtar juna da fadada hadin gwiwa. (Fa'iza Mustapha)