Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou, ya halarci bikin kammala wannan aiki a jiya Lahadi, wanda ya gudana a birnin Yamai fadar mulkin kasar.
A jawabin da ya gabatar, Mahamadou Issoufou ya ce, birnin Yamai da kewayensa na fuskantar matsalar karancin wutar lantarki, kuma wannan sabuwar cibiya da kamfanin Sin ya gina na da babbar ma'ana, wajen magance matsalar a wasu sassan kasar. Shugaba Issoufou ya yi godiya game da sahihin hadin-gwiwar dake tsakanin Sin da Nijar, gami da matukar kokarin da ma'aikatan kasar Sin suka yi wajen gina wannan katafaren aiki.
A nata bangaren kuma, ministar makamashin Jamhuriyar Nijar Amina Moumouni ta bayyana cewa, gwamnatin kasar na maida hankali sosai kan gina ababen more rayuwar jama'a a fannin makamashi, kuma wannan cibiyar samar da wutar lantarki ta Gorou Banda zata taka muhimmiyar rawa, wajen sassauta matsalar wutar lantarki dake addabar Nijar, da kawo alfanu ga al'umma, matakin da zai yi babbar ma'ana ga ci gaban tattalin arziki na Jamhuriyar Nijar. (Murtala Zhang)