in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Niamey: An bude dandali kan shimfida zaman lafiya ta hanyar tattaunawar addinai a cikin shiyyar ECOWAS
2016-11-23 10:45:02 cri

Ilimantawa kan shimfida zaman lafiya ta hanyar tattaunawa tsakanin addinai na sahun gaban wani dandalin gamayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) tun daga ranar Talata a Niamey, babban birnin kasar Nijar, a karkashin jagorancin shugaban kasar Mahamadou Issoufou.

Wannan muhimmiyar haduwa da ta kasance ta farko irinta za ta kwashe kwanaki biyu. Kuma ta samu halartar tawagogin kasashe goma sha biyar mambobin kungiyar ECOWAS da muhimman shugabannin addinai daban daban.

A cewar shugaba Mahamadou Issoufou, a yayin bude taron, wannan dandali ya zo daidai da lokacin da yankin Sahara, musammun ma yankin tafkin Chadi yake fama da barazanar ta'addanci. A cikin wannan shiyya, mutane na kashewa, na yin fyade da lalata dukiyoyin jama'a da sunan addinin musulunci. Haka kuma ana cin karo da yadda mutane suke amfani da sauran addinai domin biyan bukatunsu na siyasa, tattalin arziki da na jama'a, in ji shugaban Nijar.

Ya zama wajibi, a cewarsa, a bangaren yankin ECOWAS a yi nazari kan ba da horo ga aikin shimfida zaman lafiya ta hanyar tattaunawa tsakanin addinai.

Wannan dandali, a cewar ministan al'adun kasar Nijar, Assoumana Malam Issa, na da manufar tabbatar da ci gaban tattalin arziki da dunkulewar jama'a na kasashe mambobi goma sha biyar na kungiyar ECOWAS, yankin dake fama a halin yanzu da rikice-rikice da tashe-tashen hankalin siyasa, al'umma, kabilu da addinai, lamarin dake kawo jinkiri ga yunkurin wannan kungiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China