A jiya Litinin ne, shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar ya bayyana cewa, an samu sakamako da yawa sakamakon hadin gwiwar moriyar juna a tsakanin Nijar da kasar Sin, kuma akwai makoma mai kyau a gare su. Ya ce, kasarsa tana son hada kai da kasar Sin wajen daga huldar abokantaka da hadin gwiwa a tsakaninsu zuwa sabon matsayi.
Shugaban na Nijar ya fadi haka ne yayin da Zhang Lijun, sabon jakadan kasar Sin a Nijar ya mika masa takardarsa ta aiki a wannan rana. Shugaba Issoufou ya yi masa maraba, tare da bayyana cewa, a shekaru da dama da suka wuce, kasar Sin na tsayawa tsayin daka wajen bude kofa ga ketare da yin gyare-gyare a cikin gida, lamarin da ya raya tattalin arzikinta da rayuwar al'ummarta cikin sauri. Shugaba Issoufou ya yi imani da cewa, kasar Sin za ta kara samun ci gaba a nan gaba. (Tasallah Yuan)