in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan Boko Haram sun kai hari a wani kauyen da ke Nijar
2017-01-02 12:44:24 cri

Ma'aikatar tsaron kasar Nijar ta sanar a jiya Lahadi 1 ga wata cewa, 'yan kungiyar Boko Haram sun kai hari kan wani kauyen dake lardin Diffa, a kudancin kasar a daren ranar 31 ga watan Disambar da ya shude, inda sojojin kasar 2 suka rasa rayukansu. Kafin aukuwar harin da 'yan sa'o'i, shugaban kasar Mahamadou Issoufou, cikin jawabinsa na murnar sabuwar shekara, ya yi kira ga mayakan kungiyar ta Boko Haram da su kwance damara.

A ranar 27 ga watan Disambar da ta gabata, ma'aikatar harkokin cikin gidan jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa, matasa 30 da a baya ke cikin kungiyar ta Boko Haram sun mika wuyansu ga rundunar tsaron kasar, wadda aka jibge a lardin Diffa, domin neman lafiya, inda ake sa ran sake mayar da su cikin al'ummar kasar bayan daukar wasu matakai.

Tun daga karshen watan Yulin da ya shude ne dai rundunar sojin hadin gwiwar kasashen Najeriya, Nijar, Chadi da Kamarun, suka soma farautar ''yan kungiyar ta Boko Haram, a yankin bakin iyakar Najeriya da Nijar. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China