Rahotanni sun ce, an ji karar bindigogi babu tsayawa, kana 'yan bindigan sun gudu bayan da suka kai harin, gami da kone wata motar dakarun tsaro kurmus.
A wani labari daga jami'an tsaron Jamhuriyar Nijar kuma, gwamnatin kasar ta aike da wasu jiragen sama masu saukar ungulu daga birnin Yamai a safiyar jiya Litinin, domin bankado maboyar wadanda suka kai wannan hari.
A 'yan kwanakin nan, yankin yammacin Nijar dake bakin iyakokin kasashen Mali da Burkina Faso, na shan fama da hare-haren ta'addanci, abun da ya sa gwamnatin Nijar ta sanar da ayyana dokar ta baci a wasu jihohi shida dake yankunan Tillabery da Tahoua.(Murtala Zhang)