Bankin duniya: Nijar ta sami ci gaba kan kyautata yanayin harkoki a shekarar 2016
Kasar Nijar ta aiwatar a wannan shekara da babban ci gaba ta fuskar kyautata yanayin harkoki, tare da kasancewa kasa ta 150 bisa 190 tare da sakamako na maki 10 idan aka kwatanta da matsayinta na kasa ta 160 a shekarar 2015, a cewar rahoton "Doing Business" karo na 14 da bankin duniya ya gabatar a ranar Talata da yamma a cibiyar wakilinsa dake birnin Yamai.
A cewar sakatare-janar na ma'aikatar kasuwancin Nijar, Abdoulaye Garba, wannan kwazo da aka samu na da nasaba da sauye sauyen da gwamnatin kasar ta aiwatar a bangaren masana'antu.
A tsawon shekarar 2015, kusan kimanin kudin Sefa biliyan 526 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 875 gwamnatin Nijrar ta zuba domin kyautata yanayin harkoki a dukkan fadin kasar, a cewar faraministan Nijar, malam Brigi Rafini. (Maman Ada)