in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta mika wa kasar Nijar kayayyakin abinci kyauta
2017-03-21 20:05:48 cri

A jiya Litinin a birnin Yamai, fadar mulkin kasar Nijar, aka kaddamar da bikin mika kayayyakin abinci na tallafin kasar Sin ga gwamnatin jamhuriyar Nijar, inda jakada Zhang Lijun na kasar Sin dake Nijar din, da ministan harkokin wajen kasar Nijar malam Ibrahim Yacouba, suka rattaba hannu kan takardar mika kayan.

Bisa bayanin da sashen tattalin arziki da cinikayya na ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Nijar ya fitar, an ce za a rarraba wadannan kayayyakin abinci ne, wadanda suka hada da shinkafa ton 5547, ga iyalai fiye da dubu 50, kimanin mutane dubu 400, wadanda suke zaune a manyan yankunan kasar 8.

Jakada Zhang Lijun ya bayyana cewa, bayan da gwamnatin Nijar ta fitar da rokonta na bukatar kayayyakin abinci ga kasashen duniya, gwamnatin kasar Sin ta hanzarta daukar matakin tattara shinkafa, domin karfafa zumuncin da ya dade yana wanzuwa tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare, malam Yacouba cewa ya yi, bangaren kasar Sin ya mayar da martani ga kiran neman kayayyakin jinkai da Nijar ta yi ba tare da bata lokaci ba, kuma Sin ta samar da kayayyakin taimako cikin kankanen lokaci. Sakamakon hakan, da sahihiyar zuciya, gwamnatin janhuriyar Nijar ke godewa taimakon da bangaren Sin ya samar wa al'ummar ta. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China