in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin gwamnatin Iraki sun sake kwato unguwa ta farko a yammacin Mosul
2017-02-27 10:07:06 cri

Jiya Lahadi ne rundunar sojojin hadin gwiwa ta kasar Iraki ta sanar da cewa, rundunar sojin kasar ta sake kwato unguwa ta farko a yammacin birnin Mosul, wato yankin Mamoun.

Sanarwar ta ce, rundunar da ke yaki da 'yan ta'adda ta kasar ta shiga yankin na Mamoun ne a ranar 24 ga wata, wanda ke kuriyar kudu a yammacin birnin Mosul. Rundunar da ke yaki da 'yan ta'addan Iraki ta samu nasarar 'yantar da yankin Mamoun baki daya bayan wani kazamin fada da 'yan tawayen IS.

A ranar 19 ga watan nan da muke ciki ne, firaministan kasar Iraki Haider al-Abadi, ya sanar da kaddamar da matakin soja na sake kwato yammacin birnin Mosul. Daga baya kuma, rundunar sojin kasar ta fara kai wa 'yan tawayen IS hari. A halin yanzu, 'yan tawayen na IS kimanin dubu 3 ne suka buya a yammacin birnin na Mosul. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China