Wani babban jami'in soja daga hedkwatar da ke jagorantar hare-haren da sojojin ke kaiwa ya bayyana cewa, 'yan sandan gwamnatin tarayya, gami da rundunar sojojin ko-ta-kwana dake karkashin ma'aikatar harkokin cikin gidan Iraki, sun fara kai wani hari kan filin saukar jiragen saman Mosul tare da wani sansanin soja dake hannun mayakan IS.
An ce, harin da aka kai a safiyar wannan rana, shi ne matakan sojan na farko da gwamnatin Iraki za su dauka domin kwace ikon yankunan yammacin birnin Mosul daga mayakan IS. A halin yanzu, akwai mayakan IS da dama, wadanda suke kokarin janyewa daga wannan yanki zuwa tsakiyar birnin Mosul.(Murtala Zhang)