Rahotanni na cewa Iraqi ta bukaci mambobin kasashe 5 dake da kujerun din-din-din a M.D.D. da sauran kasashen duniya da dama, da su tsaya matsayi guda, na yin alla-wadai da Turkiyya. A sa'i daya kuma, Iraqi ta bukaci kungiyar AL da ta shirya taron ministocin harkokin kasashen wajen kungiyar don tattauna wannan batu, tun bayan da Turkiyya ta yi shisshigi a yankin kasar Iraqi, ta yadda za cimma ra'ayi guda game da wannan kutse da Turkiya ta yi cikin kasashen Larabawa.
A yayin wani taron manema labarai da shugaban Turkiyya Erdogan ya yi, tare da shugaban Bosnia-Herzegovina Dragan Covic da ya kai ziyara a kasar, ya ce, sojojin Turkiyya da ke birnin Mosul sojoji ne da ke samar da horo, sabo da haka, ba za su janye su daga kasar Iraqi ba. Erdogan ya ce, Turkiyya ta jibge sojojinta a yankin arewacin kasar Iraqi ne domin biyan bukatun da gwamnan jihar Mosul ya gabatar. Tun daga shekarar 2014 ne, Turkiyya ta fara horar da sojojin Kurdawa a kasar Iraqi.(Bako)