Rahoton ya ce, kungiyar IS ta kan yi garkuwa ko kisan gilla ga wadanda suke adawa da kungiyar, ko jami'an gwamnatin Iraqi, da sojoji, 'yan jaridu da likitoci, kana kungiyar IS ta kan kashe wadanda ke adawa da akidunsu. Rahoton ya ce, har zuwa yanzu, ana tsare da jama'a kimanin dubu 3.5 mabiya darikar Yazidi, tare da muzguna musu.
A lardunan Anbar da Ninewa, an sanya yara aiki soji. Rahoton ya ce, an kai wasu daga cikinsu zuwa sansanin horaswa dake kasar Siriya, don koya musu amfani da makamai, da yaki da fursunoni.
M.D.D. ta ce, wadannan aika-aikar sun keta dokokin kasa da kasa, kuma wasu daga cikinsu laifuffukan yaki ne da kisan kiyashi.(Bako)