Rahoton da Jaridar La Tribune ta kasar Faransa ta wallafa, ya ce shimfida wannan babbar hanya ta kunshi matakai biyu.
A mataki na farko, za'a shimfida hanya mai tsawon kilomita 1028, daga birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire zuwa birnin Ikko, inda a mataki na biyu kuma, za'a gina hanya mai tsawon kilomita dubu 3 daga Abidjan zuwa Dakar. (Murtala Zhang)