in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECOWAS ta gaza sanya shugaban Gambia sauka daga mukaminsa
2017-01-14 13:00:26 cri
A jiya Juma'a ne shugaban wakilan Kungiyar ECOWAS kuma Ministan harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama, ya ce ayarin da yake jagoranta, bai cimma yarjejeniyar da zai kai shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ga sauka ba.

Sai dai, ya ce har yanzu ba a gama tattaunawa ba, domin a yayin taron shugabannin kasashen kungiyar da aka yi a baya-bayan nan, kungiyar ta ba su umarnin cimma yarjejeniyar da zai kai shugaban ga sauka.

Cikin wakilan da suka kai ziyara Banjul babban birnin kasar Gambia har da shugabar Liberia kuma shugabar kungiyar ta ECOWAS, Ellen Johnson Sirleaf da tsohon shugaban kasar Ghana John Mahama, inda kuma suka yi ganawar sirri a lokuta mabanbanta da shugaba Jammeh da kuma zababben shugaban kasar Adama Barrow.

Geoffrey Onyeama, ya musanta rahoton dake cewa sun gaza, yana mai cewa, suna fatan samun sakamako da zai yi daidai da kundin tsarin mulkin Gambia da kuma muradin al'ummar kasar.

A nasa bangare, Mai magana da yawun zababbaben shugaban kasar Adama Barrow, Halifa Sallah, ya tabbatar da cewa har yanzu ana ci gaba da kokarin cimma yarjejeniya, inda ya ce suna fatan kokarin na wakilan ECOWAS zai dore, domin warware matsalolin da ke akwai.

Wakilan na ECOWAS tare da zababben shugaban Gambia dai sun bar Banjul jiya da dare, suka nufi Bamako babban birnin kasar Mali, inda za su halarci taron da za a yi tsakanin kasashen Afrika da Faransa a yau Asabar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China