Cikin wata sanarwa da ya fitar shugaban kungiyar ta ECOWAS, ya bukaci kasashen duniya dasu dauki matakan dakile hare haren da masu ikirarin yin jihadi suke kaddamarwa.
Sojojin 12 sun gamu da ajalinsu ne, bayan da maharan su kusan 40 dauke da muggan makamai suka afkawa sansanin sojojin dake Nassoumbou, a kusa da kan iyakar kasar da Mali.
Sakamakon harin, shugaban kasar ta Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore, ya soke ziyarar aiki da ya shirya kaiwa Najeriya, wanda da farko ya so halartar taron shugabannin kasashe mambobin ECOWAS karo na 50.