in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECOWAS na neman tayar da kalubalen shige da fice cikin 'yanci na kayayyaki a cikin shiyyar
2016-09-29 10:41:11 cri

Kwamishinar gamayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) dake kula da ababen more rayuwa, madam Antoinette Weeks, ta bayyana a ranar Laraba, shiyyar hukumarta na tayar da kalubalen shige da ficen kayayyaki a cikin shiyyar.

Muhimmin kalubale shi ne bullo da nagartattun matakai da tsari domin shige da fice cikin 'yanci na kayayyaki, in ji madam Weeks a yayin da take magana a albarkacin wani taron daidaitawa na masu ruwa da tsaki wajen aikin kula da hanyoyi a yammacin Afrika.

A cewarta, abubuwan da aka gina da wadanda ake da su dake shafar musamman ma hanyar Abidjan da Lagos sun kasance masu muhimmanci da kuma bayyana dalillan ganin wata makoma mai haske.

Ya kamata a dubi hanya a matsayin wani muhimmin ginshikin ci gaban tattalin arziki domin shiyyar kana ba kawai wani aiki guda ba na shirin gina wata hanyar mota. Ya kamata kuma mu tabbatar da cewa, gina wannan hanya na daidai da hangen shugabannin kasashe, in ji madam Weeks.

Wannan haduwa ta tattara kwararrun kungiyar ECOWAS, abokan huldar ci gaba, wakilan kasashen shiyyar, hukumomin kwastan da hukumomin karbar haraji. A cewar masu shiryawa, haduwar na da manufar tattauna wata hanya mafi daidaituwa bisa halartar kowa a cikin kulawa da hanyoyi a yammacin Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China