in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin dake Nijeriya ya mika takardar kama aiki ga shugaban kwamitin kungiyar ECOWAS
2016-10-29 12:54:20 cri

A jiya Juma'a, jakadan Sin dake Nijeriya, kuma jakadan Sin dake kungiyar ECOWAS Zhou Pingjian, ya mika takardar kama aiki ga shugaban kwamitin kungiyar ECOWAS Marcel Alain de Souza, tare da yin shawarwari da juna.

Jakada Zhou, ya nuna yabo ga kungiyar ECOWAS game taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga kasashe membobin kungiyar da su raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma, da kiyaye zaman lafiya, da raya tsarin bai daya a yankin, kana ya bayyana cewa, Sin ta dora muhimmanci sosai ga raya dangantakar dake tsakaninta da kungiyar ECOWAS, tana son ci gaba da yin hadin gwiwa, da nuna goyon baya ga kungiyar ECOWAS wajen inganta ayyukanta, da kuma raya dangantakarsu zuwa wani sabon mataki.

A nasa bangare, Marcel Alain de Souza, ya yi maraba da jakada Zhou da ya zama jakadan Sin dake kungiyar ECOWAS, da nuna yabo ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen yammacin Afirka, kana ya nuna godiya ga kasar Sin game da samar da goyon baya da gudummawa wajen raya ayyukan kungiyar ECOWAS, kana ya bayyana cewa, kungiyar ECOWAS da Sin suna da kyakkyawar makomar hadin gwiwa, yana fatan za su kara yin hadin gwiwa a fanonin samar da ayyukan more rayuwa, da zuba jari, da hada hadar kudade da dai sauransu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China