in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECOWAS ta bukaci 'yan Gambia su zama masu kishin kasarsu
2017-01-08 13:34:46 cri
Shugabar kungiyar raya cigaban tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) Ellen Johnson-Sirleaf, ta bukaci al'ummar kasar Gambiya dasu dauki darasi daga takwarorinsu na kasar Ghana, kana su sa kishin kasa sama da bukata ta kashin kai

Ghana ta gudanar da babban zabenta ne a watan Disamba cikin kwanciyar hankali, sannan a jiya Asabar ne aka gudanar da bikin rantsar da sabuwar gwamnatin da aka zaba cikin lumana, a yayin da a kasar Gambiya, al'amura suka sha bamban, bayan da shugaban kasar mai ci Yahya Jammeh yayi amai ya lashe, inda ya canza aniyarsa ta amincewa da shan kaye a zaben wanda da farkon ya ambata cewa ya fadi a zaben shugaban kasar da aka gudanar a bara, daga bisani ya bayyana cewa akwai kura kurai a sakamakon da hukumar zaben kasar ta sanar.

A wani sakon neman zaman lafiya da ta gabatar, Johnson-Sirleaf, tace ECOWAS tana fuskantar turjiya a Gambia, bayan da shugaba Jammeh, wanda ke mulkin kasar a tsawon shekaru 22 da suka gabata, ya gabatarwa kotun kolin kasar korafinsa wanda ake saran zata fara nazarin sauraron karar a ranar 10 ga wannan wata.

Johnson-Sirleaf, wacce kuma ita ce shugabar kasar Liberia, tace tuni kungiyar ta ECOWAS ta fara lalibo bakin zaren warware wannan matsala kuma shugaban Najeria Muhammadu Buhari shine ke jagorantar tattaunawar warware dambarawar siyasar ta Gambiya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China