Taron ya shafi batun kafa wani kamfanin shiyya na sufurin jiragen ruwa na ECOWAS mai suna "Sealink" domin saukaka musanya da sufuri a cikin wannan shiyya, ta hanyar rage lokacin jiran jiragen ruwa da kayayyakin da suke dauke da su a cikin tashoshin jiragen ruwa. (Maman Ada)