A jiya Laraba shugaba Hery Rajaonarimampianina na kasar Madagascar, ya yi kira ga jama'ar kasarsa da kada su manta da tarihi, su yi koyi da yaran dake tattare da kishin kasa.
Shugaban ya fadi haka ne a birnin Moramanga da ke gabashin kasar, a yayin wani gangami da aka yi, domin murnar cika shekaru 70 da yin juyin juya hali, don yakar mulkin mallaka da kasar Faransa ta yi wa kasar (Tasallah Yuan)