in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane biyu sun mutu a sakamakon fashewar bom a lokacin bikin murnar kafuwar kasar Madagascar
2016-06-27 13:07:26 cri
Firaminstan kasar Madagascar Solonandrasana Mahafaly Olivier ya bayyana a ranar 26 ga wata cewa, an samu fashewar bom a yayin bikin murnar ranar kafuwar kasar a birnin Antananarivo a wannan rana da dare, lamarin ya haddasa mutuwar mutane 2 tare da raunatar mutane kimanin 72.

Mahafaly ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyara ga mutanen da suka ji rauni a sakamakon fashewar bom din a asibiti dake cibiyar babban birnin kasar. An ce, an riga an kai dukkan mutane 72 da suka ji rauni zuwa wannan asibitin, don samun jinya.

Mahafaly ya ce, an samu fashewar bom din ne a yayin bikin nuna fasahohi na murnar ranar kafuwar kasar a filin wasa dake cibiyar babban birnin kasar, kuma an dasa bom din ne a dandalin wasan.

Mahafaly ya bayyana wannan hari a matsayin na ta'addanci, kana ya bayyana cewa, gwamnatin kasar ta riga ta dauki matakan na gaggawa don tabbatar da tsaron jama'a.

Don taya murnar ranar kafuwar kasar Madagascar, an yi bikin fareti a safiyar ranar 26 ga wata, kuma an yi bikin nuna fasahohi da yammacin wannan ranar har zuwa dare. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China