in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Madagascar ya gana da ministan harkokin waje na Sin
2017-01-08 13:59:25 cri

A jiya Asabar 7 ga wata, shugaban kasar Madagascar Hery Rajaonarimampianina ya gana da ministan harkokin wajen Sin Wang Yi a fadar shugaban kasar da ke a birnin Antananarivo.

A yayin ganawar, shugaba Hery ya bayyana cewa, Sin ta bayar da gudummawa da dama ba tare da son kai ba ga Madagascar cikin dogon lokaci. Kamfanonin Sin da yawa sun shiga aikin bunkasa kasar Madagascar, tare da ba da gudummawa sosai. Kasar tana maraba da nuna goyon baya ga kiran da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi na "Ziri daya da hanya daya", da fatan wannan kiran zai shiga sauran kasashen Afirka daga Madagascar.

A nasa bangare, minista Wang ya isar da gaisuwar shugaba Xi ga shugaba Hery, kuma ya taya kasar Madagascar murna wajen samun sulhu da tabbatar da zaman lafiya a fannin siyasa, da kuma kama hanyar samun ci gaba a cikin 'yan shekarun da suka gabata. Bayan haka, Wang ya kara da cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 45 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Madagascar. Ana fatan bangarorin biyu za su yi shawarwari da kuma tabbatar da hanyar da za a bi wajen raya dangantaka da yin hadin gwiwa tsakaninsu bisa wannan zarafi.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China