in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya bikin tunawa da kulla hulda tsakanin Sin da Madagascar shekaru 45 da suka wuce
2017-03-28 10:32:54 cri
Hadaddiyar kungiyar sada zumunta da kasashen waje ta jama'ar kasar Sin da ofishin jakadancin kasar Madagascar dake kasar Sin sun shirya wani bikin liyafa na hadin gwiwa don tunawa da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen 2 shekaru 45 da suka wuce, a jiya Litinin, a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A wajen bikin, shugaban kasar Madagascar Hery Rajaonarimampianina, da mataimakin shugaban zaunannen kwamitin na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin mista Qiangba Puncog sun yi jawabi.

Cikin jawabinsa Qiangba Puncog ya ce, cikin shekaru 45 da suka wuce, an samu nasarori masu yawa bisa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Madagascar. Zuwa yanzu, kasar Sin ta kasance kasar da ta fi cinikayya da kasar Madagascar, in ji jami'in kasar Sin.

Haka zalika, jami'in ya kara da cewa, zuwa watan Mayun bana, za a shirya dandalin hadin gwiwar kasa da kasa bisa manufar 'ziri daya da hanya daya' a birnin Beijing. Ta la'akari da yadda 'hanyar siliki ta teku' a tarihin kasar Sin ta shafi nahiyar Afirka, hakan ya sa kasar Sin ke maraba da Madagascar don ta halarci shirin 'ziri daya da hanya daya', tare da zamanto gada mai mihimmanci da ta hada shirin nan na raya tattalin arziki da daukacin nahiyar Afirka.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China