in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Madagascar ta karya ikon babban banki kan fitar da zinari zuwa kasashen waje
2015-08-07 10:21:42 cri

Gwamnatin Madagascar ta karya a ranar Laraba ikon babban bankin kasar kan kasuwanci da fitar da zinari waje. Wannan matakin da aka dauka a yayin zaman taron ministoci na ranar Laraba ya bude wata dama ga 'yan kasuwa masu zaman kansu fitar da zinari zuwa kasashen waje, in ji ministan ma'adinai da man fetur a karkashin fadar shugaban kasar, Joeli Valerien Lalaharisaina.

Babban bankin zai cigaba da kasuwanci da fitar da zinari zuwa kasashen waje a Madagascar amma kuma su ma 'yan kasuwa masu zaman kansu na iya gudanar da harkokinsu a wannan fanni yanzu, in ji minista Joeli Valerien Lalaharisaina .

Amma duk da haka, ana son da farko bullo da matakai da za su rakiyar wannan shirin, wanda zai tilasta bayyana yawan ajiyar zinarin 'yan kasuwa domin gayyatarsu bin doka da oda, in ji ministan.

A cikin watan Junin shekarar 2012, gwamnati ta dauki matakin hana 'yan kasuwa fitar da zinara, amma tare da baiwa babban bankin damar yin hakan, 'yan kasuwa dama sun rika samun zinari ta kasuwannin bayan fage da fitar da zinarin waje ba bisa doka ba, in ji mista Lalaharisaina.

A cewar babban taron MDD kan kasuwanci da cigaba na CNUCED, kilogram 600 na zinari, wanda aka kisata darajarsa zuwa dalar Amurka miliyan 18, aka fitar ba bisa doka ba daga Madagascar tsakanin shekarar 2012 da 2013. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China