Wang Yi ya bayyana haka ne a yayin da yake ganawar 'yan jarida bayan shawarwari a tsakaninsa da takwararsa ta Madagascar madam Béatrice Atallah a birnin Antananarivo, inda ya kuma kara da cewa, makasudin kiran da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi na raya "Ziri daya da hanya daya" tare, shi ne neman samun ci gaba da annashuwa da kasashen dake amincewa da wannan tunani ta hanyar yin shawarwari da bunkasuwa tare. Kawo yanzu, kasashe da yankuna sama da 100 ne suka mai da martani cikin yakini, tare da samun sakamako mai kyau.
Ban da haka, Wang Yi ya bayyana cewa, nahiyar Afirka wani muhimmin kashi ne na hanyar siliki a yankin teku a tarihi, ita ce wuri mafi nisa a yamma, kuma muhimmin wuri ne da aka nufa. Idan kasashen Afirka suna fatan shiga shirin "Ziri daya da hanya daya", ba shakka ana maraba sosai. A hakika dai, kasar Sin ta riga ta yi shawarwari da kasashen Afirka da yawa, musamman ma kasashen dake gabashin nahiyar, tare da samun ci gaba. Ya ce an yi imani cewa, tare da zurfafuwar hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, nahiyar Afirka za ta kara samun moriya a fannin bunkasuwa.
Dadin dadawa, Wang ya ce, a ziyararsa a wannan karo, kasashen Sin da Madagascar sun yi shawarwari kan aikin "Ziri daya da hanya daya", tare da cimma matsaya daya.(Fatima)