Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce har kullum kasar Sin na dora muhimmanci kan raya hulda a tsakaninta da kasar Koriya ta Kudu, tana kuma mu'amala da gwamnatin kasar, da ma sassa daban daban na kasar, yayin da a daya hannun ma'aikatun harkokin wajen kasashen 2 ke ci gaba da tuntubar juna yadda ya kamata.
An labarta cewa, kasar Sin na nuna adawarta da shirin jibge makamai, karkashin tsarin kandagarkin makamai masu linzami da ake kira THAAD a Koriya ta Kudu. Game da hakan ne ma a kwanan baya, kasar ta Sin ta tuntubi jam'iyyun 'yan hamayyar kasar a maimakon mahukuntan kasar, a wani mataki da gwamnatin Sin ta fara dauka na samun mafita. (Tasallah Yuan)