Mr. Hong ya bayyana hakan ne a gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, inda aka tambaye shi cewa, cinikayyar da ke tsakanin Sin da Koriya ta arewa ya kai kashi 90 cikin dari na jimillar kudin cinikayya tsakanin kasar Koriya ta Arewa da sauran kasashen duniya, wanda hakan ya sanya kasar ta Sin babban nauyin gudanar da kudurin mai lamba 2270.
A game da tambayar, Hong Lei ya amsa da cewa, makasudin kuduri mai lamba 2270 a bayyane yake, wato dasa shinge, da kuma dakatar da shirin Koriya ta Arewa na samar da makaman nukiliya masu linzami, amma ba tare da kawo illa ga rayuwar jama'ar kasar, da kuma bukatun su na jin kai ba.
Ya ce cikin kudurin, an bukaci sake farfado da shawarwari tsakanin bangarori shida, da sassauta yanayin da ake ciki a arewa maso gabashin Asiya ta hanyar siyasa da diplomasiyya da dai sauransu. Wannan ce muhimmiyar hanya ta daidaita batun nukiliya a zirin Koriya. Shi ya sa ya dace a gudanar da wannan kuduri cikin daidaito a dukkanin fannoni. Ya ce bai kamata a mai da hankali kan wani fanni kawai tare da kyalle sauran fannnoni ba. (Fatima)