in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Zimbabwe ba zai nada sabon shugaban jam'iyya mai mulki ba
2017-02-26 17:07:01 cri

Shugaban kasar Zimbabwe kuma shugaban jam'iyyar ZANU-PF dake mulkin kasar Robert Mugabe, ya bayyana a jiya 25 ga wata cewa, ba zai nada sabon shugaban jam'iyyar ba. A cewarsa, za a yi zaben sabon shugaban ne yayin taron wakilan jam'iyyar da zai gudana a shekarar 2019.

Shugaba Mugabe wanda ya halarci bikin ranar haihuwarsa ta cika shekaru 93 da aka gudanar a wurin shakatawa na Matobo dake da nisan kilomita 40 daga birnin Bulawayo na kasar, ya bayyana cewa, ya kamata a gudanar da dukkan harkokin jam'iyya bisa kundin tsarin jam'iyya. Kuma bisa kundin, kuma za a samu sabon shugaban ne ta hanyar yin zabe a wajen taron wakilan jam'iyya, a maimakon shi da kansa da ya nada, inda ya ce nadawan da kanshi, sabawa kundin tsarin jam'iyyar ne.

Bugu da kari, Mugabe ya bayyana cewa, tilas ne sabon shugaban jam'iyyar ya kasance kwarare a dukkan fannoni da kuma gudanar da ayyuka bisa biyayya ga dokokin jam'iyyar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China