Ta ce ana samun karuwar adadin wadanda suke aikata laifin, inda a bara aka yankewa mutane hamsin da bakwai hukuncin zaman gidan yari na akalla shekara tara, tana mai cewa, ko a shekarar 2015, an yi ta samun matsalar, inda aka kame tare da tura mutane da dama gidan yari.
A kalla 'yan asalin kasar dari hudu da arba'in da hudu tare da 'yan asalin kasar Zambia talatin da 'yan Mozambique bakwai da kuma wani dan kasar Afrika ta kudu ne aka kama da laifukan da suka shafi kashe namun daji.
Washaya-Mayo ta ce ana zargin ayarin na Zimbabwe da ketare iyaka da giwaye ta tsaunin Zambezi dake yankin arewacin kasar yayin da 'yan kasar Mozambique suka bi ta tsaunikan Gonarazhou da Save.
Ta kara da cewa, bullo da dabarun zamani na yaki da wannan mummunar dabi'a, da ya hada da amfani da jirage marasa matuka da karnukan farauta, zai taimaka gaya wajen magance matsalar farautar dabbobin daji ta haramtacciyar hanya a yankunan da aka kebe da iyakoki. ( Fa'iza Mustapha)