in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe ta tabbatar da fitar da giwaye 35 zuwa ga Sin
2017-01-06 13:57:13 cri
Jiya Alhamis, hukumar kula da lambun shan iska gami da namun daji ta kasar Zimbabwe ta tabbatar da cewa, kasar ta fitar da giwayen Afirka guda 35 zuwa kasar Sin a ranar 23 ga watan Disambar da ta gabata.

Mai magana da yawun hukumar Madam Caroline Washaya-Moyo ta shaidawa 'yan jaridu cewa, an samo wadannan giwaye ne daga wani lambun shan iska dake arewa maso yammacin kasar Zimbabwe.

Hukumar kula da lambun shan iska gami da namun daji da wasu kungiyoyin kyautata yanayin namun daji, sun gudanar da bincike sosai kan wuraren da za'a ciyar da wadannan giwaye a Sin.

A cewar Madam Moyo, jami'an Zimbabwe sun gudanar da bincike daga dukkanin fannoni a wasu gidajen namun daji dake biranen Beijing, Shanghai, da Hangzhou na kasar Sin, wato inda za'a ajiye wadannan giwaye a nan gaba, kuma sakamakon binciken ya gamsar da su.

Madam Moyo ta kara da cewa, za'a yi amfani da daukacin kudin shigar da aka samu daga fitar da giwayen a fannin kare namun daji, kuma ayyukan fitarwa gami da jigilar giwayen, sun dace da yarjejeniyar kasa da kasa kan cinikin halittun abubuwa da suke bacewa gami da ka'idojin ciniki da yin jigilar dabbobi masu rai da aka cimma tsakanin Sin da Zimbabwe.

A ranar 29 ga watan Disambar bara, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta bayyana cewa, fitar da giwaye zuwa kasar Sin da kasar Zimbabwe ta yi, cinikayya ce wadda ta dace da yarjejeniyar kasa da kasa da dokokin kasashen biyu.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China