Haq ya fadawa 'yan jaridu a wannan rana cewa, Guterres ya sake nanata cikakken goyon-bayansa ga Staffan de Mistura, wanda shi ne wakili na musamman kan batun rikicin Siriya, domin gudanar da shawarwarin lami-lafiya.
Haq ya kuma bayyana cewa, MDD na maida hankali sosai kan barazanar tsaro da matakan soja da ake dauka a Al-Raqqah ka iya haifarwa fararen-hula sama da dubu dari hudu. MDD kuma ta ce, bangarori daban-daban suna da nauyin kare fararen-hula gami da na'urorinsu bisa dokar kasa da kasa.
An fara shawarwari a sabon zagaye kan batun Siriya dake karkashin jagorancin MDD a birnin Genevaa ranar 24 ga watan nan, wanda ya kasance zagaye na biyar da aka shirya shawarwarin tsakanin wakilan gwamnatin Siriya da na dakarun dake adawa da gwamnati.(Murtala Zhang)