Ya kara da cewa, za kuma a gudanar da wani sabon zagayen tattaunawar bayan wasu kwanaki, a cikin watan nan da muke ciki.
A cewar mista Mistura, duk da cewa ba a samu wani muhimmin sakamako yayin tattaunawar ba, tawagar gwamnatin kasar Syria da masu adawa da gwamnatin, sun cimma matsaya kan abubuwan da za su tattauna a kai a zaman da za a yi nan gaba.
Hakan a cewar Mistura ya shimfida wani kyakkyawan tubali ga tattaunawar da za a gudanar a nan gaba.
Ban da haka kuma, mista Mistura ya ce abubuwan da za a tattauna kansu a nan gaba, sun kunshi batutuwa 4. Cikinsu har da batutuwa 3 da suka shafi mika mulkin kasar, wato su kafa gwamnatin gamin gambiza da gyara kundin tsarin mulki da sake gudanar da babban zabe. Ban da haka kuma aka kara da batun yaki da ta'addanci, bisa bukatar tawagar jami'an gwamnatin kasar Syria.(Bello Wang)