Mr. Xie ya bayyana haka ne a jiya, yayin wani taron manema labarai da aka kira a fadar Palace of Nations, inda ya ce, tattaunawa domin neman sullhu maimakon matakan soji, ita ce hanyar daidaita rikicin Syria.
Ya ce, Kamata ya yi a samar da yanayin da ya dace da tsagaita bude wuta, sannan, a inganta aikin tsagaita bude wuta ta hanyar yin shawarwari.
Ya kara da cewa, yana fatan masu ruwa da tsaki za su tabbatar da gudanar da tattaunawar yadda ya kamata, sannan su nemi cimma daidaito duk da bambancin da suke fuskanta, inda ya yi kira da a fara daga matsaloli masu sauki, don a samu amincewa da juna.
Mr. Xie Xiaoyan ya ce, ya kamata a bar jama'ar Syria su yanke shawara kan makomarsu, haka kuma, ya kamata gwamnatin da masu adawa da ita su yi hakuri da juna su kuma tattauna domin kokarin cimma wani shirin da zai dace da moriyar al'umma. (Lubabatu)