Dakarun gwamnatin Syria sun kwace iko da garin Khafseh da tasoshin ruwa dake yammacin gundumar Aleppo na arewacin kasar, biyo wata gumurzu da 'ya'yan kungiyar IS.
Jaridar Al-Watan mai goyon bayan gwamnatin Syria da ke wallafa labaranta a kafar intanet, ta ruwaito cewa, kwato garin na Khafseh daga hanun kungiyar IS na da matukar muhimmanci, la'akari da cewa, yankin ya kunshi koramu dake samar da ruwan sha ga birnin Aleppo.
Kimanin makonni 8 ke nan al'ummar Aleppo miliyan 1.5 ke fuskantar rashin ruwan sha, tun bayan da kungiyar IS ta yanke hanyar isar ruwan sha birnin.
Rahoton Jaridar ya bayyana cewa, murna ta barke a birnin Aleppo, sanadiyyar kwato garin da kuma sa ran dawowar ruwan sha nan bada dadewa ba.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Syria, ta tabbatar da kwato garin Khafseh mai tasoshin ruwa dake gabar kogin Euphrate. (Fa'iza Mustapha)