A cikin wasikar, ma'aikatar harkokin wajen Syria ta ce, an kai wadannan farmakin ne har sau biyu, domin mayar da martani kan nasarar da sojojin gwamnatin kasar suka samu wajen murkushe kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi a wasu wurare na kasar, a daya bangaren kuma, hare-haren sun nuna cewa, kungiyoyin ta'addanci dake kasar Syria na adawa da yunkurin neman sulhu.
An kai harin na Birnin Damascus din ne a jiya, kan wasu motoci biyu dauke da fararen hula 'yan darikar Shi'a na Iraki, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 40, yayin da mutane sama da 120 suka ji rauni.
Rahoton da Gidan rediyon the pan-Arab al-Mayadeen na kasar Lebanon ya bayar na cewa, tuni kungiyar 'yan tawaye ta Levant Swords dake da nasaba da 'yan tawaye dake adawa da gwamnatin Syria wato Free Syrian Army ta dauki alhakin kai harin. (Bilkisu)