Rahotanni sun bayyana cewa, tuni gwamnatin kasar ta kara sojojin da ta tura zuwa wuraren dake kusa da Jobar, inda kuma aka toshe wasu hanyoyin da za su isa yankin.
Kungiyar kare hakkin bil Adama wadda hedkwatarta dake birnin London na kasar Burtaniya, ta bayyana cewa, 'yan tawayen sun harba boma-bomai a wurare da dama dake birnin Damascus, sa'an nan sojojin gwamnatin kasar sun mai da martani gare su ta sama.
Rahotannin sun kara da cewa, yayin gumurzun, sojojin gwamnati sun kashe 'yan tawayen da dama, tare da jikkata wasu. (Maryam)