A ranar Asabar da ta gabata ne, an aka kai harin bom ga wasu manyan motoci 2 masu dake dauke da fasinjoji 'yan darikar Sshi'a na kasar Iraki, a birnin Damascus, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane fiye da goma.
Dangane da hare-haren, ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta mika sako ga babban magatakardan MDD da shugaban kwamitin sulhu na Majalisar, inda ta bukaci Majalisar da ta yi tofin Allah tsine kan wadannan hare-haren bom da suka abku a Damascus. A cewar ma'aikatar, an kai hare-haren ne don ramuwar gayya ga sojojin gwamnatin kasar, wadanda sakamakon suka samu nasarorin da suka samu a kwanakin baya wajen tinkarara a yakin da suke yi da kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi a kwanakin baya. Haka zalika, hare-haren sun nuna yadda 'yan ta'adda dake kasar ba sa son ganin samun masalaha tsakanin al'ummomin kasar, in ji ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria.(Bello Wang)