in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar EU ta kulla sanarwar Rome
2017-03-26 13:36:35 cri
Jiya Asabar 25 ga wata, an kammala taron kolin kungiyar tarayyar kasashen Turai ta musamman watau taron cika shekaru 60 wajen kulla yarjejeniyar Rome a babban birnin kasar Italiya, Rome, inda aka kuma kulla sanawa ta Rome.

Cikin sanarwar din, an bayyana cewa, a halin yanzu, kasashen Turai suna fuskantar kalubaloli da dama da suka hada da rikicin dake tsakanin sassa daban daban a yankin, hare-haren ta'addanci, matsalar 'yan gudun hijira, kariyar ciniki da kuma rashin daidaituwa wajen raya tattalin arziki da dai sauransu. Shi ya sa, ana sa ran mambobin kungiyar EU za su yi hadin gwiwa da kuma mutunta ka'idodjin da aka kulla tare, ta yadda za a karfafa karfin kungiyar EU da kuma inganta fahimtar juna a tsakanin mambobin kungiyar.

Haka zalika, sanarwar ta ce, cikin shekaru goma masu zuwa, za a dukafa wajen gina kungiyar EU zuwa wata wadattaciyar kungiya mai tsaro, mai zaman karko da kuma mai saurin bunkasuwar tattalin arziki, ta yadda za a samu dauwamammen ci gaba da kuma ba da gudummawa ga zaman takewar al'umma yadda ya kamata. Kana, ana fatan kungiyar EU za ta ba da muhimmin tasiri kan harkokin kasa da kasa.

Ban da kasar Burtaniya, shugabannin mambobin kungiyar EU guda 27 da wasu shugabannin hukumomin kungiyar sun halarci taron da aka yi a birnin Rome.

A ranar 1 ga watan nan da muke ciki, shugaban kwamitin kungiyar EU Jean Claude Juncker ya gabatar da takardar ci gaban EU bayan ficewar kasar Burtaniya daga kungiyar, a yayin cikakken zaman taron majalisun dokokin kasashen Turai da aka yi a birnin Brussels na kasar Belgium, inda ya yi bayani kan dabaru guda biyar kan yadda za a gina kungiyar EU mai mambobi guda 27 a shekarar 2025, lamarin da ya zama tushe na tattaunawar dake tsakanin shugabannin kungiyar kan yadda za a nemi bunkasuwar kasashen Turai a yayin taron kolin din da aka yi a birnin Rome. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China