Gwamnatin kasar Burtaniya ta bayyana cewa, za ta fara aiwatar da shirin ficewa daga kungiyar EU kafin karshen watan nan da muke ciki, wannan ya sa aka mai da hankali matuka kan takardar da kungiyar EU ta fidda.
Kamar yadda ke kunshe cikin dokar kungiyar EU, Burtaniya za ta fara shirin ficewa daga kungiyar bayan da majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar yin hakan. Kasashe 27 ne za su rage a cikin kungiyar bayan kasar Burtaniya ta fita daga kungiyar a EU. (Maryam)