Wannan mataki na nufin, firaministar kasar za ta fara shiri da kuma yin shawarwari da kungiyar EU bayan ta sami izni daga sarauniyar kasar Burtaniya.
A wannan rana da dare ne, majalisar dokokin ta yiwa muhawara kan daftarin dokoki guda biyu da ta fitar game da ficewar kasar daga kungiyar EU. Kana kafin a kada kuri'u a majalisar dattijai kan wannan batun, an kuma kada kuri'u a majalisar wakilan kasar, inda aka tabka muhawara kan daftarin guda biyu, lamarin da ya nuna cewa, majalisar dattijai ta nuna hakuri da majalisar wakilan, inda aka kuma zartas da daftarin ficewar kasar Burtaniya daga kungiyar EU.
A farkon watan nan da muke ciki ne, majalisar dattijai ta yi muhawara game da zartas da daftarin ficewar kasar daga kungiyar EU, sa'an nan, ta bukaci gwamnati da ta yiwa fannoni biyu na daftarin gyaran fuska wadanda suka hada da kare 'yancin al'ummar kungiyar EU dake zaune a kasar Burtaniya yadda ya kamata, da kuma tabbatar da 'yancin majalisar dokokin kasar na tsai da kuduri kan ko kasar Burtaniya za ta iya ficewa daga kungiyar EU ko a'a. (Maryam)