Shugaba Erdogan ya bayyana haka ne a yayin wani taron dandalin tattaunawa da aka yi a birnin Antalya dake kasar. Ya ce, za a kada kuri'a kan harkokin gyara tsarin mulkin kasa a ranar 16 ga watan Afrilu mai zuwa. Bayan haka kuma, mai yiwuwa ne, za a kada kuri'a kan ko kasar za ta ci gaba da neman shiga kungiyar EU, ko a'a.
Sabo da aikin kada kuri'a kan gyaran tsarin mulkin kasa da za a yi a wata mai zuwa, gwamnatin kasar Turkiya za ta tura jami'ai zuwa kasar Jamus da Holland da dai sauran kasashe, domin sa kaimi ga 'yan kasar Turkiya wadanda suke zaune a kasashen da su jefa kuri'ar, amma, wasu kasashen kungiyar EU sun ki shigar da wadannan jami'an Turkiya, lamarin da ya tsananta huldar dake tsakanin kasar Turkiya da kasashen.
Dangane da wannan batu, shugaban kasar Turkiya Recep Erdogan ya bayyana a ran 23 ga wata cewa, kasar Turkiya za ta sake dudduba dangantakar siyasa dake tsakaninta da kunigyar EU, ciki har da yarjejeniyar yadda za a tsugunar da 'yan gudun hijira wadda aka kulla a tsakanin kasar Turkiya da kungiyar EU. (Maryam)