in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya da Tarayyar Turai sun ratabba hannu kan yarjejeniyar inganta kiwon lafiya a kasar
2017-02-17 10:18:37 cri
A jiya Alhamis ne Nijeriya da Tarayyar Turai EU, suka rattaba hannu kan wata yarjeniya, ta dalar Amurka miliyan saba'in da hudu, da nufin samar da ingantaccen kiwon lafiya da sinadaran gina jiki a jihohi biyar na Kasar tare da kuma yaki da cutar shan inna.

Yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar a Abuja babban birnin kasar, shugaban tawagar kungiyar a Nijeriya Micheal Arrion, ya ce EU ta dauki batun tallafawa bangaren lafiya a Nijeriya da muhimmanci.

Ya ce cikin yarjejeniyar, an jadaddda muhimmancin inganta kula da lafiyar mata da kananan yara tare kuma da karfafa tsarin kiwon lafiya, ta yadda za a rika bibiyar kiwon lafiyar al'umma a ko da yaushe, da nufin shiryawa tinkarar duk wata annoba da ka iya barkewa.

Ya bayyana karfafa tsarin kiwon lafiya a matsayin muhimmin batu da ya janyo cimma yarjejeniya da asusun raya kasashe na kungiyar EU na 11 wato EDF, da kungiyar EU da Nijeriya suka ratabbawa hannu .

A cewarsa, asusun ya ware dala miliyan dari biyar da hamsin da biyar, domin tallafawa Nijeriya a cikin shekaru biyar, inda kuma cikin wannan kudi ne aka bada tallafin miliyan saba'in da hudu na aiwatar da wannan yarjejeniya.

Ya kara da cewa, karkashin asusun EDF na 11, EU da Nijeriya na aiki tare wajen magance kalubalen ci gaba a muhimman bangarori. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China