A ranar 13 ga wata, Nicola Sturgeon ta bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, tana fatan sake kada kuri'a kan neman 'yancin kai na Scotland a tsakanin watan Yuli na shekarar 2018 zuwa watan Maris na shekarar 2019.
Dangane da wannan batu, firaministar Burtaniya Theresa May ta bayyana a ran 16 ga wata cewa, idan za a kada kuri'a kan neman 'yancin kai na Scotland, lamarin zai haddasa matsala ga kasar yayin shawarwari game da ficewar kasar daga kungiyar tarayyar turai EU, kuma wannan ba abu ne mai adalci ga al'ummonin Scotland ba, saboda an bukace su da su tsai da irin wannan kuduri mai muhimmanci a lokacin da ba su san wane irin dangantaka da za a kulla da kungiyar EU ba, har ma, ba a tabbatar musu wace irin makoma za su samu ba bayan samun 'yancin kai na Scotland. (Maryam)