in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an Sin da na Burtaniya sun tattauna batun tsaro
2017-02-20 11:20:39 cri
An gudanar da taron shawarwari kan batun tsaro tsakanin manyan jami'an kasashen Sin da na Burtaniya karo na 2 a birnin London na kasar Burtaniya a ranar Jumma'a da ta gabata, inda babban sakataren kwamitin shari'a na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, mista Wang Yongqing, da mai ba da shawara ga firaministar kasar Burtaniya kan batun tsaro Mark Grant, sun jagoranci taron shawarwarin.

Yayin tattaunawarsu, manyan jami'an bangarorin Sin da Burtaniya sun nuna yabo kan sakamakon da aka samu ta fuskar hadin gwiwar bangarorin 2, bayan an gudanar da taron shawarwari tsakaninsu a karon farko a watan Yuni na bara.

A yayin taron na wannan karo, jami'an bangarorin Sin da Burtaniya, sun yi musayar ra'ayi kan batutuwan da suka shafi yakar ta'addanci, da masu tsattsauran ra'ayi, da tabbatar da tsaron shafunan yanar gizo na Internet, da dakile gungun baragurbi masu aikata laifuka, da maganar tsaro a wurare daban daban dake janyo hankalin dukkan bangarorin 2.

Bisa tattaunawar da suka yi, manyan jami'an kasashen Sin da Burtaniya sun cimma daidaito, kan yadda za a gudanar da hadin kai tsakanin kasashen 2, musamman ma a fannonin tinkarar barazanar ta'addanci, da dakatar da yaduwar ra'ayin ta'addanci ta hanyar shafin yanar gizo, da tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen sama masu dauke da fasinjoji, da dai makamantansu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China