A watan Janairu, a lokacin da take ziyarar aiki a kasar Amurka, firaministar kasar Burtaniya Theresa May ta sanar da cewa, sarauniyar kasar Elizabeth II ta gayyaci shugaba Trump da ya kai ziyarar aiki a kasarta a hukumance, sa'an nan, Mr. Trump ya karbi gayyatar da sarauniya ta yi masa. Amma, ba da dadewa ba, majalisar dokokin kasar Burtaniya ta sami wata takardar roko da 'yan kasar sama da miliyan 1.8 suka sa hannu, inda suka yi kira da a soke gayyatar da sarauniyar ta yiwa Donald Trump.
Kuma, bisa ka'idar da abin ya shafa, idan adadin mutane da suka sa hannu kan takardar roko ya wuce dubu 100, ya kamata a yi tattaunawa kan batun da abin ya shafa a majalisar dokokin kasar, amma, gwamnatin kasar Burtaniya ta sanar a watan jiya cewa, kasar ba za ta soke gayyatar da aka yiwa shugaba Trump ba. (Maryam)